<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Ya Uba Na Cikin Sama, Ina Roƙonka LW40</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Uba na cikin Sama, ina roƙonka,
 Bisa ga alkawarinka, ji addu'ata.

[V2]
 KORUS
 Yesu, Yesu, ji addu'ata,
 Ina zuwa wurin Uba cikin sunanka.

[V3]
 2) Uba, ga ni nan gabanka, na yi zunubi.
 In ba za ka karƃe ni ba, wa zai taya ni?
 Korus

[V4]
 3) Cikin ƙasar can mai nisa, na yi baƙunci,
 Amma dai yanzu na komo, sai ka karƃe ni.
 Korus

[V5]
 4) Ni ban isa ba ka ji ni, Allah Ubana,
 Amma cikin sunan Yesu, kawo gafara.
 Korus

[V6]
 5) Uba, ina yin godiya, kai ka karƃe ni.
 Ka maishe ni bawa naka, aikinka in yi.
 Korus</lyrics>
<hymn_number>40</hymn_number>
</song>